africa

‘Yan sandan Najeriya sun yi arangama da ‘yan IPOB a kudancin kasar


'Yan sanda
Bayanan hoto,

Rundunar ‘yan sandan ta jima ta na fafatawa da ‘yan aware na kungiyar IPOB da ke kudancin Najeriya.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Imo a kudu maso gabas ta ce ta kashe wani babban kwamandan ‘yan a-ware na ƙungiyar IPOB mai fafutukar kafa ƙasar Biafra.

Ta ce an kashe Joseph Uka Nnachi wanda aka fi sani da suna Dragons ne a jiya Lahadi lokacin da suka yi yunƙurin far wa hedikwatar ‘yan sanda a birnin Owerri.

A jihar Delta ma ‘yan bindiga ne suka ƙona wani ofishin ‘yan sanda a ƙaramar hukumar Ndokwa ta gabas tare da ƙona wata mota, ko da yake babu rahoton wanda ya rasa ran shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo SP Bala Elkana ya fadawa BBC cewa ‘yan bindigar waɗanda ‘yan kungiyar IPOB ne, sun shirya kai hare-hare kan manyan gine-gine gwamnati ciki har da hedikwatar ‘yan sanda.READ SOURCE

Leave a Reply

This website uses cookies. By continuing to use this site, you accept our use of cookies.  Learn more