africa

Tinubu da Shekarau: Abubuwan da manyan ‘yan siyasar suka tattauna


Tinubu da Shekarau

Asalin hoton, Tinubu Media

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu da tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau sun gana a karon farko tun bayan rikici ya barke a jam’iyyar tasu reshen jihar Kano.

Rikicin , wanda ya sa Shekarau da wasu ‘yan majalisar dokokin tarayya na jihar ta Kano ballewa daga bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka kira kansu G-7, ya kuma sa bangarorin biyu kowanne ya gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar na jiha.

A bangaren Gwamna Ganduje, an zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano, yayin da a bangaren Sanata Shekarau aka zabi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar.

Wadannan zabuka sun raba kawunan ‘yan jam’iyyar ta APC a a jiar Kano, wadda ta fi yawan al’umma a arewacin Najeriya. Hasalima rikicin ya kai ga Ganduje da Shekarau suna yi wa juna shagube.READ SOURCE

Leave a Reply

This website uses cookies. By continuing to use this site, you accept our use of cookies.  Learn more