africa

Omoyele Sowere da Burna Boy: Abin da ya sa suke cacar-baki kan Fela Anikulapo Kuti


Sowere da Burna Boy

Mai fafutukar mulkin dimorkradiyya Omoyele Sowore da fitaccen mawakin nan dan Najeriya Burna Boy sun barle da cacar baki bayan da mamallakin jaridar intanet ta Sahara reopters ya gayyaci mawakin domin shiga zanga-zanga.

Lamarin ya faru ne bayan Sowere ya aike da sakon Twitter ga Burna Boy inda ya bukace shi ya bi sahunsa wajen gudanar da zanga-zanga ta ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.

“Zuwa ga @burnaboy, duk inda na duba mutane sun bayyana ka a matsayin mawaki mai ra’ayin kawo juyin juya hali, kafafen watsa labaran kasashen waje suna jinjina maka suna kwatanta ka da Fela Kuti, amma ban taba ganin ka jagoranci kowa ba domin zuwa ofishin ‘yan sanda dauke da akwatin gawa kan shugaban kasa. Ka zo mu shiga zanga-zangar ranar #Oct1stProtest #RevolutionNow.”

Sai dai mawakin ya yi wa Sowere raddi inda ya ce bai yarda da ‘yan siyasa ba yana mai cewa su ne suka jefa Fela cikin rigimar da ta yi sanadin rayuwarsa.

“Kowanne mutum yana ikirarin zama masoyin Fela kuma mai goyon bayansa yanzu da yake ya mutu. Dan Adam yana da ban dariya, dukkanku ‘yan siyasa halayenku guda (musamman a Najeriya) kuma a gaskiya ban yarda da ku ba,” a cewar Burna Boy.

Wadannan kalamai sun jawo ce-ce-ku-ce daga magoya bayan ra’ayoyin da mutanen biyu suka bayyana, kuma hakan ne ya sa suka kasance batun da aka fi tattaunawa a shafin Twitter a safiyar yau Laraba.

Hasalima mamallakin jaridar Sahara Repoters din ya bukaci Burna Boy ya tambayi dan gidan Fela, Femi Kuti, domin sanin irin rawar da ya taka wajen kare muradun fitaccen mawakin.

Amma Burna Boy ya ce: “Ni ba FELA ba ne. Na sha fadar haka sau tarin masaki. Amma kai dan siyasa ne, don haka kar ka saka ni cikin tsare-tsarenka.”

Mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan takaddama tsakanin Mr Sowere da Burna Boy inda suka goyi bayan wanda suke ganin ya fi gaskiya.

Wani mai sharhi a Twitter, Dr. Dípò Awójídé ya bayyana cewa: “Burna Boy ba ya son rigima da hukumar tsaro ta farin kaya DSS. Ya fi so ya yi wakarsa, ya tafi London a cikin jirginsa sannan ya yi hira da manema labarai a kan juyin juya hali, a matsayinsa na gwarzon Afirka da kuma yadda mu matsorata ba za mu iya kalubalantar gwamnati ba. Shi kuma Sowore yana son rigima da DSS.”

Kauce wa Twitter, 3

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3

Shi kuwa Ayo Sogunro cewa ya yi yana mamakin game da yadda wasu ke yi wa Burna Boy kallo a matsayin mai fafutuka kawo sauyi.

“Abu daya da ya sauya kawai shi ne salon waka,” in ji shi.

A nasa bangare, Olumuyiwa ya ce ba dole ba ne sai Burna Boy ya shiga zanga-zanga domin kuwa bai ci bashin kowa ba.

“Burna Boy ba shi da nauyin kowa na gudanar da zanga-zanga. Nauyin da ya rataya a wuyansa shi ne ya daina yin abubuwan da za su nuna cewa ya fi mu son kawo sauyi domin ya fake da son Fela.

Kauce wa Twitter, 5

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 5

Shelar kifar da gwamnati

A baya 2019, jami’an hukumar tsaron ta farin kaya wato DSS, sun kama Omoyele Sowore, mai kamfanin jaridar Sahara Reporters ta intanet kan shelar da ya yi ta #RevolutionNow da ke nufin juyin juya-hali.

A wancan lokacin, mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya ce suna da cikakkiyar masaniya kan ‘goyon bayan’ da Mista Sowore yake samu daga kasashen waje da nufin tayar da tarzoma a Najeriya ta hanyar shelar da ya yi ta ‘samar da sauyi a kasar’.

READ SOURCE

Leave a Reply

This website uses cookies. By continuing to use this site, you accept our use of cookies.  Learn more