africa

Nasiru Kachalla: Abu biyar kan ƙasurgumin mai satar mutanen da aka kashe a Kaduna


Nasiru Kachalla

Bayanan hoto,

Nasiru Kachalla ya daɗe yana kai hare-hare da satar mutane a wasu yankunan jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani ƙasurgumin ɗan fashi kuma mai satar mutane da ya addabi jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar a ranar Litinin, ya ce an kashe Nasiru Kachalla ne a wani artabu tsakanin ɓangarorin ƴan bindigar biyu da suka addabi yankunan Kajuru da Chikun.

Mista Aruwan ya ce ƙungiyoyin wasu mutane da ke bayar da bayanan sirri sun tabbatar wa da gwamnatin cewa faɗan ya jawo an kashe miyagun da dama na dukkan ɓangarorin biyu, da suka haɗa da manyan yaran Kachalla.

An yi wannan artabu ne a wani daji da ke iyakar ƙananan hukumomin Kajuru da Chikun, kuma “mummunan rikicin” ya samo asali ne kan wasu garken shanu da suke taƙaddama a kai.READ SOURCE

Leave a Reply

This website uses cookies. By continuing to use this site, you accept our use of cookies.  Learn more