Na yi luwadi ne don layar da boka ya bani ta fara aiki – Tsoho mai shekaru 58


– A ranar Laraba ne jami’an tsaro suka damke wani mutum mai shekaru 58 a duniya a kan zargin shi da ake da yin luwadi da wani matashi mai shekaru 20

– Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Haruna Mohammed ya ce wanda ake zargin ya yi hakan ne don tsafin kudi

– An mika lamarin zuwa fannin binciken laifuka na jihar don tsaurara bincike, kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda John Abang ya bada umarni

A ranar Laraba ne jami’an tsaro suka damke wani mutum mai shekaru 58 a duniya a kan zargin shi da ake da yin luwadi da wani matashi mai shekaru 20.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, lamarin ta faru ne a karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da kamen. Ya kara da cewa wanda ake zargin ya yi hakan ne don tsafin kudi.

Ya ce, “A ranar 8 ga watan Afirulun 2020 wajen karfe 1 na yamma, jami’an tsaro da ke yankin Nnewi sun kai wa wani Josephat Unachukwu mai shekaru 58 samame.

“Sun kuwa yi nasarar damke shi a yankin Edoji Uruagu da ke karamar hukumar Nnewi ta jihar Anambra.

“Ana zargin shi da lalata wani matashi ne mai shekaru 20 don layar da wani matsafi ya bashi ta fara aiki.”

Na yi luwadi ne don layar da boka ya bani ta fara aiki - Tsoho mai shekaru 58

Na yi luwadi ne don layar da boka ya bani ta fara aiki – Tsoho mai shekaru 58
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Tallafin man fetur: Kyari ya yi bayani game da janye tallafi da FG tayi

Kamar yadda kakakin ya bayyana, an mika lamarin zuwa fannin binciken laifuka na jihar don tsaurara bincike, kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda John Abang ya bada umarni.

READ  Kenya police help colleagues escape anti-graft officers with warning shots

A wani labari na daban, A ranar Laraba ne aka gurfanar da wasu matasa uku a gaban kotun majistare dake Ile-ife a jihar Osun.

An zargi matasan ne da satar dan kamfai da rigar nono na mata wadanda aka yi amfani dasu, jaridar The Nation Online ta ruwaito.

‘Yan sandan sun zargi Ofelola Olawuyi mai shekaru 25, Ajayi Damilare mai shekaru 27 da kuma Toheeb Elugbaju mai shekaru 19, da laifuka uku.

Laifukansu sun hada da satar dan kamfai da rigar nono, rashin ladabi da kuma hada kai wajen cutarwa.

Lauyan masu gurfanarwa, Emmanuel Abdullahi ya sanar da kotun cewa wadanda aka gurfanar din sun aikata laifin ne tsakanin 6 zuwa 7 ga watan Afirilun 2020 da misalin karfe 9 na safe a Ile-Ife.

Abdullahi ya zargi wadanda aka gurfanar din da yin abinda zai kawo rashin zaman lafiya da tashin-tashina.

Ya sanar da kotun cewa, a lokacin da aka kama wadanda ake zargin, sun kasa bada gamsassun bayanai a kan dalilin da yasa aka samu dan kamfai da rigunan nono na mata a tare dasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

READ SOURCE

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here