africa

Mohammed Bello Matawalle: Ana ce-ce-ku-ce kan yunkurin komawar Gwamnan Zamfara APC


Mohammed Bello Matawalle

Asalin hoton, Zamfara State Government

Ana ci gaba da muhawara kan sauyin sheƙar da Gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle zai yi nan gaba zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

An shafe tsawon lokaci ana yaɗa jita-jitar cewa gwamnan yana shinshina jam’iyya mai mulki kafin APC ta tabbatar da komawarsa a ƙarshen mako.

Sai dai a iya cewa yayin da APC ta shirya gagarumar tarba kan wannan ƙaruwa da ta samu, sauyin sheƙar ga alama ya tayar da ƙura mai girman da ba san lokacin lafawar ta ba a nan gaba.

Rahotanni masu ƙarfi na cewa a ranar Talatan nan ne ake sa ran gwamnan zai sauya sheƙa daga jam’iyyar siyasa ta PDP zuwa ta APC.READ SOURCE

Leave a Reply

This website uses cookies. By continuing to use this site, you accept our use of cookies.  Learn more