
Asalin hoton, Getty Images
Masu zanga-zanga sun kusa cikin ginin majalisar
Rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan Shugaba Turmp na Amurka da ke zanga-zanga da kuma ƴan sanda a ranar Laraba lokacin ƴan majalisar dokokin ƙasar ke taron haɗin gwiwa don tabbatar da nasarar Joe Biden.
Taron ƴan majalisar ya gamu da cikas sakamakon ɓarkewar rikici tsakanin ƴan sanda da masu zanga-zanga a cikin ginin majalisar wato Capitol.
Bayan jerin zanga-zangar da aka yi kan adawa da dokar kullen korona, da suka haɗa da na Michigan inda masu ta da zaune tsaye suka kutsa majalisar jihar, a yanzu kuma ga irin hakan na faruwa a babban birnin Amurkan Washington DC.
Trump ya shafe makonni yana iƙirarin cewa shi ne ya lashe zaɓen ƙasar, inda ya ce an yi maguɗi a manyan jihohin da Biden ya yi nasara ba tare da ya gabatar da wata hujja ba.
Shi da magoya bayansa sun yi ta matsa wa mataimakinsa Mike pence kan ya sauya sakamakon zaɓen ta hanyar ƙin tabbatar da nasarar Biden, wani abu da ƙwararru suka ce ba shi da ƙarfin iko a shari’ance na yin hakan.
A kwanakin da suka gabata kafin ranar tabbatarwar, Trump ya ce zai halarci taron gangamin “Save America” wato “A ceci Amurka” da za a yi ranar Laraba a birnin Washington, inda ya yi alƙawari a Twitter cewa gangamin zai kasance babba kuma gagarumi.
Sa’a guda bayan da Trump ya yi wa dubban mutane jawabi tare da alƙawarin cewa ba zai taɓa amsa shan kaye ba, sai rikici ya ɓarke.
Me ya faru a cikin majalisar?
Asalin hoton, Getty Images
‘Yan sanda sun yi ta watsa hayaƙi mai sa hawaye
Kafafen yada labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa an yi ta watsa hayaƙi mai sa hawaye a cikin ginin majalisar yayin da mutanen da ke kutsawa ciki ke ƙaruwa.
Ƴan sandan da ke cikin Majalisar Taryyar Amurkan sun kama wasu daga cikin masu zanga-zangar, yayin da wasu daga cikinsu ke ci gaba da shiga ginin majalisar.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun haura bango inda suka afka ciki, amma tuni ƴan sanda suka ciro bindigoginsu da kuma barazanar harbin masu zanga-zangar.
An cewa ƴan majalisa da manema labarai da ke cikin ginin majalisar su fice su nemi maɓoya tare da sanya takunkumin da zai kare su daga shaƙar hayaƙi mai sa hawaye.
Masu zanga-zangar sun ci gaba da kutsawa cikin ginin Capitol, wasu na ta ɗaukar hotuna.
Wasu kuma suna ihun “Trump muke so” ta yadda ƙarar tasu ta karaɗe wajen, yayin da ake ta ƙoƙarin nemar wa ƴn jarida da ƴan majalisun mafaka.
Me Trump ya ce?
Asalin hoton, Getty Images
“Ku yi komai cikin nutsuwa,” in ji Trump
Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kira ga magoya bayansa da su bi komai a sannu a yayin da suka dirar wa Majalisar Dokokin ƙasar wato Capitol.
Ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa “su bi doka da odar majalusar.”Tabbas suna bayan ƙasarmu ne,” kamar yadda ya rubuta.
“Ku yi komai cikin nutsuwa.”
Tuni shi ma magajin garin birnin Washington Muriel Bowser ya yi umarnin sanya dokar hana zirag-zirga da za ta fara aiki da misalin ƙarfe 6 na marecen ƙasar.
Me Mike Pence ya ce?
Matamakin shugaban ƙasa ya yi kira ga masu goyon bayan Trump da su bar ginin na Capitol tare da dakatar da rikicin.
“Ba za mu lamunci wannan hari a kan majalisarmu ba, kuma za a tuhumi duk wanda aka kama da laifi,” a cewar Mike Pence.
Tun da fari dai mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya ce ba zai hana tabbatar da nasarar Joe Biden a zaben shugaban kasa ba, a yayin zaman hadin gwiwar na majalisun kasar.
Sai dai ya ce zai bai wa masu son kalubalantar zaben dama su bayyana ra’ayoyinsu kan nasarar da Mista Biden ya samu, abin da a bisa al’ada wani karamin al’amari ne, sai dai ga alama karamar magana ta zama babba.
Shugaba Donald Trump tun da farko ya bukaci Mista Pence da ka da ya tabbatar da sakamakon yayin zaman majalisun, sai dai Shugaban Majalisar Dattijan Mitch McConnell, ya fada wa majalisar cewa babu wata hujja da ke nuna cewa an aikata wani abu da zai sauya sakamakon zaben.
Ya ce: “Babu wani abu da aka kawo gaban mu dake nuna an yi ba dai-dai ba a ko ina da da ya kusa zama wani gagarumin abu, wani gagarumin abuda zai kawo wa daukacin zaben tawaya”.