africa

Ibrahim Gambari: ‘Yan fashi ‘sun yi yunkurin fasa gidan shugaban ma’aikatan fadar Buhari


Ibrahim Gambari

Asalin hoton, Getty Images

Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da abin da ta kira yunkurin da wasu suka yi na fasa gidan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ranar Litinin.

A wata sanarwa da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce wasu sun yi yunkurin fasa gidan Farfesa Ibrahim Gambari da misalin karfe uku na dare.

Gidan nasa yana kusa da fadar shugaban kasa, a cewar sanarwar.

Sai dai Garba Shehu ya ce yunkurin nasu “bai yi nasara ba.”READ SOURCE

Leave a Reply

This website uses cookies. By continuing to use this site, you accept our use of cookies.  Learn more