africa

Dangote da BUA: Ganduje ya sasanta manyan masu kuɗin Najeriya biyu


Ganduje da BuA da Dangote

Asalin hoton, Kano Govt

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sasanta tsakanin hamshaƙan ƴan kasuwar Najeriyar nan biyu ƴan asalin jihar, Alhaji Aliko Ɗangote da Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u kan saɓanin fahimtar da suka samu a baya-bayan nan.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamnan Ganduje ya ce an yi zaman sulhun ne tsakanin jami’an gwamnatin jihar da wasu manyan masu faɗa a ji da kuma ƴan kasuwar ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce rikicin na baya-bayan nan ya samo asali ne tsakanin manyan masu arzikin biyu kan batun farashin sikari a kasuwar Najeriya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Dangote ya zargi BUA da amfani da wata dama ta hanyar da ba ta dace ba, yayin da shi kuma Abdussamad ya ce yana so ya mamaye kasuwar ne ya kuma dinga sa farashi yadda ya ga dama.READ SOURCE

Leave a Reply

This website uses cookies. By continuing to use this site, you accept our use of cookies.  Learn more