africa

Bola Tinubu: Manyan ƙalubalen da ke gaban tsohon gwamnan Lagos a zaben 2023


Asiwaju Bola Ahmad Tinubu

Asalin hoton, TINUBU

Matakin da jagoran jam’iyyar APC a Najeriya kuma tsohon gwamnan Legas Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ɗauka na bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2023 wata alama ce da ke nuna cewa an buga kugen siyasa yayin da ake tunkarar zaɓe mai zuwa.

An daɗe ana raɗe-raɗin cewa Tinubu zai tsaya takarar shugaban ƙasa, sai dai ya furta hakan da bakinsa a fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan ya gana da shi ranar Litinin.

Tinubu dai babban mai fada a ji ne a jam’iyyar APC, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen nasararta a zaɓukan 2015 da kuma 2019, kana ya samu damar kafa yaransa na siyasa da dama a wurare daban-daban waɗanda su ma a yanzu sun samu ƙarfin iko a jam’iyyar, wani abu da ake ganin zai taimaka masa.

Sai dai duk da waɗannan damarmaki da mutumin da ake kira Jagoran APC ke da su, wasu masana harkokin siyasa na ganin cewa akwai wasu manyan ƙalubale da ka iya yi masa tarnaƙi wajen cikar burin da ya shafe tsawon rayuwarsa yana fatan cikarsa, kamar yadda ya bayyana da bakinsa.READ SOURCE

Leave a Reply

This website uses cookies. By continuing to use this site, you accept our use of cookies.  Learn more