africa

Biden ya fara aiki domin sauya dukkan manufofin gwamnatin Trump


US President Joe Biden signs documents after being sworn-in

Bayanan hoto,

Shugaba Biden bai bata lokaci ba wajen sanya hannu kan dokokin da za su dakatar da alkiblar Amurka kan sauyin yanayi da bambancin launin fata

Shugaban Amurka Joe Biden ya fara kwance dukkan ayyukan mutumin da ya gada Donald Trump, ana sa’o’i kalilan bayan ya sha rantsuwa.

“Babu lokacin da za mu bata kan batutuwan da ke fuskantar mu,” kamar yadda ya sanar a wani sakon Twitter yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Fadar White House ji kadan bayan an ransar da shi.

Shugaba Biden ya sanya hannu kan wasu dokokin shugaban kasa 15, ta farkonsu ita ce wadda za ta bunkasa aikin kawar da annobar korona.

Sauran dokokin sun yi watsi ne da manufofin gwamnatin Trump kan sauyin yanayi da shige-da-fice.

READ SOURCE

Leave a Reply

This website uses cookies. By continuing to use this site, you accept our use of cookies.  Learn more